Kungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS), ta ce za ta ɗora alhakin duk wasu ayyuka na take haƙƙin ɗan adam da dakarun sojin haya na Wagner suka yi dangane da rikicin jamhuriyar Nijar.
Kwamishinan harkokin siyasa, zaman lafiya da tsaro na ECOWAS, Ambasada Abdel-Fatau Musah ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels ranar Juma’a.
Musah ya ce yanzu haka dakarun na Wagner na can a ƙasar Mali, saboda akwai wani ƙulli da suka yi tsakanin gwamnatin Mali da ƙasar Rasha.
Ya bayyana cewa muddun dakarun na Wagner, waɗanda mallakin Rasha ne suka yi wani abu na take haƙƙin bil’adama, to babu wanda ECOWAS za ta ɗorawa alhakin sai ƙasar Rasha da kuma ƙasar da ta ɗauko hayarsu.
Ya ce yanzu ƙasashen Afrika ba sa buƙatar irin waɗannan dakarun na haya masu zaman kansu a nahiyar, kuma duk wani abu da suka yi, alhakin zai rataya ne a wuyan ƙasashensu na asali.
Musah ya ƙara da cewa ba za su bari Afrika ta Yamma ta zama filin da wasu ƙasashen duniya za su gwada ƙarfin makamansu ba.