Masana harkokin sufuri sun fara bayar da shawarwari ga direbobi da masu amfani da ababen hawa kan matakan da za su bi domin rage yawan man fetur din da motocinsu ke sha.
Hakan na zuwa ne yayin da gwamnatin ƙasar ta cire tallafin man fetur, lamarin da ya haddasa ƙaruwar farashin man a fadin ƙasar.
Masanan sun ce akwai buƙatar direbobi da masu amfani da ababen hawa su ɗauki matakin rage yawan man da motoci da sauran ababen hawansu ke sha, don kauce wa ƙarewar man da wuri.