Daga Jamila Sulaiman Aliyu
Kwalejin Aminu Kano hadin gwiwa da jami’ar tarayya ta dutsimma ta gudanar da bukin maraba lale na sama da dalibai dubu daya wadanda zasuyi karatun digiri a fannoni daban daban.
Shugaban makarantar Dr Ayuba Ahmad ya ce bukin maraba lalen na daliban sama da dubu daya anyishi ne ranar lahadi 16/7/2023 wadanda zasu gudanar da karatun digiri da sahalewar jami,’ar Tarayya dake dutsimma ta jihar katsina
Ya kara da cewa fannoni goma Sha daya da zasu fara karbar darasi akansu Yayin da kwalejin tayi ragin kaso arba”in da biyar na kudin makarantar domin daliban su samu saukin gudanar da Al,amuran karatunsu inda ya yi Kira ga gwamnatin Kano da ta dubi wannan makaranta ta fuskar matsuguni domin matsuguninta a yanzu haka bai wadatar ba la,akari da yadda gwamnatin kanon ke baiwa harkar ilmi mahimmanci.
A jawabin sa maimartaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayaro Wanda wakilin gabas Alhaji sani sarki yola ya wakilta ya shawarci daliban dasu Mai da hankali akan karatunsu tare da kaucewa shiga kungiyoyin Asiri da ake fama dasu a kasarnan wadanda suke dakile harkokin tsaro a makarantun
Shugaban Jami”ar Tarayya ta dutsimma farfesa Arma ya’u Bichi Wanda Dr Jamilu Ajiya ya wakilta yace sun tantance kwasa kwasai goma. Sha daya domin ayi digiri a kansu domin kwalejin ta cika ka”idojin koyo da koyarwa.
Ya Kara da janhankalin daliban da sukayi nasarar samun guraben dasu yi abin daya dace domin su cimma burin su.
Magatakardan makarantar Mr Ayola Olafemi shine ya jagoranci maraba lalen da aka yiwa sabbin daliban A jawabansu daban daban farfesa Abdallah Uba Adamu da Farfesa Abdurrashed Garba sun shawarci shugaban kwalejin akan su yi kokarin shigar da tsarin fasahar zamani a harkokin karatunsa domin bunkasa makarantar
Wasu sabbin dalibai da sukayi jawabi a madadin daliban Usman Labaran, Alawiyya Nuhu da Awwalu dawakin kudu sun bayyana farin ciki su tare da rokon abokan karatunsu dasu rungumi abin daya kawosu makarantar.