Hukumar hisbah ta shiya taron tunatarwa ga mata domin kalubalen da yake gabansu wajen kula da tsaida sallah ga ya’yayansu duba da yadda wasu iyayen ke sauke faralinsu ba tare da sun umarci iyalansu ba.
Mataimakiyar kwamandan hisbah ta karamar hukumar nassarawa malama wasila Abdullahi ce tayi tunatarwar a masallacin juma,a na hotoro wanda ya samu halattar iyaye mata da yammata masu tarin yawa.
Malamar ta tunatar dasu girman darajar da sallah take da ita wadda har ma,aiki S.A.W ya ambaceta da Ginshikin Addini.
Mataikiyar kwamandan ta kuma bayyana ire iren matsalolin da iyayen kan haifar a gidajensu inda sau tari uba ko magidanci ke daura alwalar sallah ya kuma tafi masallacin ya gabatar amma bai damu da maidakinsa da ya”yansu gudanar da sallar ba ko bai umarcesu su gabatar ba.
Ta kara da cewa yawanci uwace take sakacin umartar ya’yanta suyi sallah sai kaga suna kallo ko danne dannen waya da sauran ayyukan shagala amma uwa ko shugabar gida ta yi sallarta ba tare da ta umarcesu da suyi sallah ba
Malama wasila Abdullahi ta jawabi mai ratsa zuciyoyi a lokacin tuna tarwar har ta buga misali da cewar su iyaye madubi ne ga ya’yansu domin duk abinda iyayen suka aiwatar abin koyi yake zama ga ya’yansu don haka ta ja hankalin iyayen dasu ringa aikata alkhairi ko ya’yansu zasu yi koyi dasu.