Gwamnoni na ci gaba da fakewa a bayan talakawa domin isar da manufar su
An bayyana kokarin da gwamnoni suke yi na ganin an ci gaba da karbar takardun 500 da 1000 a matsayin hanyar neman damar amfani da miliyoyin nairorin da suka kwasa na hakkokin talakawa a wajen zabe.
Bayanin hakan na kunshe cikin jawaban da jiridar aksammedia ta samo daga al’ummar garin Kano a yayin kewayen jin ra’ayoyin al’umma
Har yanzu gwamnoni na ci gaba da kalubalantar shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Dalilan gwamnonin na cigewa akan ba sa bukatar wanzuwar tsarin takaita takardun kudade a cikin al’umma bai wuce ganin za’a dode hanyoyin da suka saba mika cin hanci ga wadanda suke son sarrafa wa ba
Rahotanni na nuni da cewa tun bayan kammala zaben fidda gwani na jam’iyyar APC da PDP na yan takarar shugaban kasa, shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi alkawarin kawo karshen siyasa sana’a
Sai dai a wancan lokacin duk da ya fadawa gwamnoni kudurin nasa amma ba su yi tsammanin faruwar hakan a daidai wannan lokaci ba.
Ka saurari jawabin shugaban kasa Muhammadu Buhari da aka fassara da hausa kaji kyawawan munufar sa da gwamnonin suke yaki da ita kuma suke fakewa a bayan talakawa.
Idan suna son Gaskiya su Bari a rika baiwa kananan hukumomi giran din su daga gwamnatin tarayya.