Har yanzu ‘yan Najeriya na cikin rudani duk da cewa shugaba Muhammadu Buhari ya yi jawabi a ranar Alhamis kan ci gaba da aiwatar da kudurin daina amfani da tsaffin takardun kudi a Najeriya tare da bada tabbacin cewa gwamnati na yi duk mai yiyuwa wajen samar da wadatattun sabbin takardun kudi.
Shugaban kasa ya kara da cewa za a hukunta duk wanda aka samu da laifin yiwa tsarin sabbin takardun kudin zagon kasa. Sai dai masu hada-hadar POS na ci gaba da cin karensu babu babbaka ganin yadda suke tsawallawa ‘yan kasa wajen cajar kudin da ake biya idan za’a cira kowanne dubu 1 a kasar, lamarin da ke kara jefa mutane cikin mawuyacin hali.
Wannan al’amari na janye tsaffin takardun kudin naira 200, 500 da 1000 daga amfani ga ‘yan kasa na ranar 10 ga watan Febrairu kafin shugaba Buhari ya sanar da dawo da amfani da naira 200 zuwa ranar 10 ga watan Afrilu na ci gaba da jawo rudani musamman ma ganin yadda rahotanni daga sassan Najeriya daban-daban suka yi ta nuni da cewa wasu gwamnonin arewa sun yi biris da jawabin da shugaba Buhari ya gabatar a ranar Alhamis suna masu umartar mazauna jihohinsu da su ci gaba da yin amfani da tsoffin takardun kudin wajen gudanar da ayyukan su na yau da kullum.
Bisa ga dukkan alamu wasu ‘yan Najeriya sun fara ganin laifin masu hada-hadar kudi ta POS cikin wadanda suke tsawallawa ‘yan kasa ta hanyar cajar kudi ba bisa ka’ida ba ga mabukata sakamakon karancin sabbin takardun kudin a bankunan kasuwanci.
Mataimakin shugaban kungiyar masu sha’anin hada-hadar kudi ta POS, Dakta Kamal Abdulkadir Musa, ya ce wahalar da mambobin kungiyarsu ke shiga wajen samun kudin na daga cikin dalilan da ya sa aka kara wani abu a farashin caji-caji da ake yi a matsayin wani kason na adadin kudin da mai bukata ya nema.
Daraktan hada hadar kudi na CBN, Mal. Ahmed Bello Umar ya shaida mana cewa gwamnati zata dauki tsauraran matakai a kan duk mai POS da aka kama da laifin zaluntar ‘yan kasa ta hanyar caje-caje da suka sabawa ka’ida.
Duk da ikirarin babban bankin Najeriya dake jadada cewa yana ci gaba da sakarwa bankunan kasuwanci kudi don rage radadin da ‘yan kasa ke ciki, ‘yan kasa na dada bayyana irin halin kakani-kayi da gwamnati ta sanya su a ciki kamar yadda da zaku ji a cikin wannan ra’ayoyi.