Kimanin marasa lafiya da dama ne su ka rabauta da tallafin kudi daga gidauniyar kabiru dalladi Bello foundation.gidauniyar da ke fadi tashi wajen tallafawa aluma musammam ma masu rangwamen karfi
Hakan yasa a wannan karon gidauniyar ta ziyarci babban asibitin kwanciyar dake karamar hukumar gwarzo Dan tallafawa marasa lafiya da zunzurutun kudade har kimanin dubu biyar biyar.
Daga Nan Kuma Gidauniyar ta Kara nikar Gari zuwa gidan ajiya da gyaran hali Dan futo da wadan da aka yiwa Tara basu da halin biya.
Wani matashi Mai suna Gali na daya daga cikin wanda ya shaki iskar yanci ya bayyana farin cikin sa da godiya bisa fitar dasu da wannan gidauniya Tayi.
Sannan ya godewa shugaban tafiyar Kabiru dalladi Bello, aluma da dama ne suka sami halartar taron zagayan.