Daga Jamila Sulaiman Aliyu
FA’IDA DAGA AL-ƘUR’ANI…14
Allah maɗaukakin Sarki Yana cewa yayin da yake bada labarin yanayin da ɗan adam zai shiga na nadama lokacin da aka nuna mishi wuta a zahiri:
{يَقولُ يا لَيتَني قَدَّمتُ لِحَياتي} سورة الفجر، آية ٢٤.
{Yana cẽwa, “Kaicona, dã na gabatar (da aikin ƙwarai) domin rãyuwata!”}. Suratul Fajri, aya ta 24.
Rayuwa ta gaskiya ita ce rayuwar lahira, domin ita ce mai tabbata har abada! Yayinda mumini ya tabbatar da hakan a zahiri zai ji ina ma bai bar wata dama ta kufce mishi ba face ya aikata abinda Allah ke so a cikinta. Shi kuwa kafiri, shi ke da babbar asara a wannan rana, domin kuwa ya rusa rayuwar gaskiya akan ta wargi!!
Lahira ita ce haƙiƙanin rayuwa, don haka mu shirya gaskiya gwargwadon hali, duk ƙanƙantar aiki kar mu raina shi, muhimmin abu dai ikhlasi, kamar yadda duk girman aiki kar mu ruɗu da shi domin da rahmar Allah ne zai zamo ya amfane mu.
🖊️Zainab Ja’afar Mahmud
20th J/Akhir 1444A.H
13th January 2023