Kungiyar yankasuwar gyada dake nan jihar kano,koka dangane da rashin tallafi daga Gwamnatocin jiha da na tarayya,bisa tallafawa ‘ya’yanta ta hanyar basu jari da zamanantar da harkokin kasuwancinsu na fannin gyada da waken suya da ma man gyadar a jihar kano.
Shugaban matasa na kungiyar Alhaji Aminu inuwa ne ya bayyana haka ga manema labarai a ofishinsa dake Tafawa balewa a karamar hukumar Nassarawa dake nan kano.
Aminu inuwa yace,akwai tallafe tallafe da Gwamnatoci suka baiwa wasu kungiyoyin a kano a matsayin tallafi ga kungiyoyi da dama, amma kungiyar yankasuwar gyada basu taba samu ba,duk gudunmawa da goyan baya da kungiyar take baiwa Gwamnatoci, musamman wajen biyan kudaden haraji da samarwa matasa domin su zamto masu dogaro da kawunansu.
Shugaban yace,jihar kano ciyace ta kasuwancinsu da yakamata Gwamnati ta bijiro da abubuwan da za ta taimakawa matasa su kaucewa zaman kashe wando da shiga ayyukan batagari da sauransu.
Aminu inuwa ya kara da cewa,harkokin kasuwancinsu ana mutukar bukatar su a koina a Duniya kasancewar sana,a ce da take bukatar Gwamnatoci, musamman ta jihar kano su kawo hanyoyin da za su bunkasata da zamanantar da kasuwancinsu domin yin gogayya da sauran kasashen Duniya.
(Inda yace hakan ba zai samu ba zai Gwamanati ta shigo ta inganta harkar domin a samu ci gaba ta fannin kasuwancin gyada da waken suya da nauin kayayyaki da ake amfani da su wajen sarrafa man da kuli kuli,Wanda ana abubuwa da dama da shi,saboda kullum ilimi yana karuwa ne)
Yace,ta fannin kasuwanci kuwa,idon aka yi duba da lokutan da suka gabata akwai sauye sauye da aka samu na farashin kayayyaki da karyewar tattalin arziki a jihar kano abune dake bukatar Gwamnatoci su shigo damin zamanantar da harkokin kasuwancinsu da kuma,basu tallafi kamar sauran kungiyoyin yankasuwa.
Haka zalika,yayi kira ga matasa da su kasance masu biyayya da dogaro da kawunansu, musamman yankungiyar kasuwar yangyada dake Tafawa Balewa,akan su ci gaba da baiwa shugabancin kungiyar domin samun bijiro da managartan abubuwan ci gaba domin inganta harkokin kasuwancinsu.
Daga karshe ya yabawa Gwamnatoci bisa gudunmawar da suke baiwa kungiyoyin yankasuwa anan jihar kano, da yin kira ga matasa da su kawo shiga cikin bangar siyasa domin su ne shugabannin gobe da za su jigoranci kasar nan.
Ibrahim sani gama pyramid.