DANTALA UBA NUHU KURA:
An Bayyana Hadin kai Da sulhu a Tsakanin Manoma Da Makiyaya a matsayin Babban abin da yake da alfanu wajan kawo zaman lafiya da dorewar arziki.
Bayanin hakan na kunshe cikin jawabin Dagacin Baure Alh Adamu Ismaila Baure a Karamar Hukumar Kura, a Yayin da ya Jagoranci Zaman Kwamitin sulhu Maisuna Gyara Kayanka Wanda Yakubu Sani Baure Ke shugaban ta.
A Cewar sa sulhun Hanyace Ta Inganta Zaman Lafiya Da Cigaba Da Samun Daidaito a Tsakanin Manoma Da Makiyaya a Karamar Hukumar Kura da jihar Kano dama Kasa Baki Daya.
    Maimagana Da Yawun Makiyayan Fulani Dantala Butalawa Gawo a Karamar Hukumar Ta Kura Ya Bayyana Hakan Bayan Kammala Zagayen Wasu Burtalai a Yankin Da Suka Hada Da Baure, Gidan Dan-Kauye, Bawa, ‘Dan-Kwashare, Da Sauran Wasu Da Gonaki Domin Shata Iyaka Da Hanyoyin Dabbobin Da Makiyayan Kebi a Yankunan
Daga karshe Butalawa ya Bayyana Godiyarsa Ga Dagacin Bisa Yadda Shugabannin Manoman Suka Bukaci Zamansu a Gidan Dagacin Dan Cinma Matsaya Da Samum Daidaito kuma ya Bayyana Wasu Hanyoyin Da Makiyayan Zasu Kaucewa Binsu Dan Samun Zaman Lafiya.
Anasa Bangaren Shugaban Kwamitin Yakubu Sani, Ya Bayyana Farincikinsa Da Samun Daidaito Da Hadinkai Da Suka Suka yi a wajan Dagacin Nasu Da Yadda Ya Hada Kan Makiyayan Da Manoman Dan Cinma Matsaya.
Tun da fari Wakilin Dagacin Baure Alh Adamu Ismaila, Yusuf Adamu Ya Yayi Karin Haske Kan Kwamitin Bisa Hadinkan Da Akasamu Tsakanin Manoma Da Makiyayan
Inda Ya Hore su su zama Masu Zaman lafiya.