Kudirin Majalisar tarayya akan CBN ya tsallake karatu na biyu

Kudirin da ke neman a rage karfin gwamnan babban bankin CBN ya tsallake karatu na biyu a majalisar dattawan.

Yan majalisa na son wani da ba gwamnan babban bankin ba ya zama shugaban hukumar CBN kuma suna so a janye ikon hukumar na tabbatarwa da kayyade albashi da alawus din mambobinta da amincewa da kasafin kudin bankin na shekara

A ranar Talata ne kudurin neman rage karfin ikon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) ya tsallake karatu na biyu a majalisar dattawa, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kudirin wanda Sanata Sadiq Umar ya shigar, ya nemi a yiwa dokar CBN mai lamba ta 7 kwaskwarima domin bayar da damar nada wani daban a matsayin shugaban hukumar gudanarwa ta bankin.
wanda ba gwamnan babban bankin ba.

A dokar ta yanzu, gwamna mai ci aka nada don zama shugaban hukumar gudanarwar babban bankin. Sauran mambobin hukumar sune mataimakan gwamnan hudu, sakataren dindindin, ma’aikatar kudi, daraktoci biyar da babban akanta janar na tarayya.

Kazalika Hukumar ke da alhakin tsarawa da gudanar da gaba daya harkoki da kasuwancin bankin, ciki harda tsarawa da aiwatar da manufofin chanjin kudi dama da amincewa da kasafin kudin bankin na shekara.

A cikin kudirin, majalisar dattawan ta kuma bukaci a janye ikon hukumar CBN na tabbatarwa da albashi ko kuma kayyade shi da alawus din mambobinta da kuma dubawa da amincewa da kasafin kudin bankin na shekara.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments