Adadin wadanda suka mutu sakamakon cutar kwalara a Malawi ya kai 183.
Ministan Lafiya na kasar, Khumbize Chiponda a cikin wata rubutacciyar sanarwar da ya fitar, ya bayyana cewa tun daga watan Maris, adadin wadanda suka kamu da cutar ya karu zuwa dubu 6 da 56 kuma adadin mutanen da suka rasa rayukansu ya kai 183.
Chiponda ya jaddada cewa barkewar cutar kwalara na afkuwa ne sakamakon matsalolin samun ruwa mai tsafta da kuma amfani da bandaki yadda bai dace ba.
Da yake lura da cewa wasu majinyata suna gujewa magani saboda dalilan addini, Chiponda ya bukaci kungiyoyin addini su gargadi jama’a.
Cutar kwalara da ta ci gaba da raguwa na tsawon shekaru sakamakon matakan da hukumomin lafiya da gwamnatocin kasashe suka dauka, ta sake fara yaduwa saboda dalilai kamar sauyin yanayi, talauci da tashe-tashen hankula.
Bisa rahoton kididdigar da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta fitar, yayin da adadin wadanda suka kamu da cutar ta kwalara a duniya bai kai kaso 20 ba daga shekarar 2017 zuwa 2021, annobar kwalara ta bulla a kasashe 26 a shekarar 2022 kawai.