Yawan al’ummar Tanzaniya, daya daga cikin kasashen gabashin Afrika, ya karu da kusan kashi 40 cikin 100 a cikin shekaru 10 da suka gabata.
Sakamakon kidayan mutanen kasa da aka yi ya nuna cewa, adadin mutanen da ke zaune a kasar mai yawan jama’a miliyan 44.9 a shekarar 2012 ya kai miliyan 61.7 a yanzu.
Yayin da mata suka kasance kashi 51 na al’ummar kasar, adadin mutanen da ke zaune a birnin Dar es Salaam, cibiyar tattalin arzikin kasar ya karu zuwa miliyan 5.4.
Yayin da al’ummar tsibirin Zanzibar suka kai miliyan 1.9, yawan mazauna babban birnin Dodoma ya kai miliyan 3.1.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa kashi 1 cikin 4 na al’ummar duniya za su kasance ne a nahiyar Afrika nan da shekarar 2050, idan aka ci gaba da samun karuwar al’umma a halin yanzu.