Yadda al’ummar Jigawa da ambaliya ta ɗaiɗaita ke kokawa kan halin da suke ciki.

Daga Walid Hari
Ɗaruruwan mutanen da suka gudu daga garuruwansu zuwa wasu yankuna masu aminci sakamakon ambaliyar ruwa a jihar Jigawa da ke Arewacin Najeriya sun koka a kan mawuyacin halin rayuwar da suke ciki.

Hukumomi dai sun tsugunar da mutanen na wucin gadi a makarantun gwamnati, inda a kan ba su taimako, yayin da akasarin su ke zaune a gidajen ƴan uwa da abokan arziki.

Wata mata da ke samun mafaka a sansanin ta ce suna fuskantar ƙalubale ta fuskar kula da lafiya amma ana ta ɓangaren ta ce ba kullum abinci ke wadatar da su ba.

Alhaji Abdulkadir Umar Bala TO, Shugaban ƙaramar hukumar Hadeja ya ce suna iya ƙoƙarinsu wajen tallafa wa mutanen.

“Gwamnati tana ba da tallafi na ɗauki sannan al’umma da ƙungiyoyi da ƴan siyasa, kowa yana kawo gudummawarsa domin tallafa wa mutanen nan.

Ya kuma musanta iƙirarin wasu da ke cewa abincin da ake ba su ba ya isarsu inda ya ce “duk zance sukeyi kawai.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments