Labarin kasuwar cefanen yan wasan kwallo kafa

Daga Walid Hari.
Chelsea ta so gwajin lafiyar da aka yi wa Christopher Nkuku ya gudana cikin sirri saboda kawo yanzu ba ta cimma matsaya ba a kan yawan kudin da za ta biya dan wasan RB Leipzig kuma dan wasan gaban Faransa mai shekara 24.(Fabrizio Romano)

Liverpool za ta fuskanci fafatawa mai zafi daga Juventus da Real Madrid wajen sayen dan wasan Belguim Youri Tielemans, mai shekara 25, wanda kwantiraginsa a Leicester zai zo kare a karshen kakar wasa ta bana.(Calciomercato – in Italian)

Sevilla da Valencia na zawarcin dan wasan gaban Faransa, mai shekara 26, Anthony Martial daga Manchester United. (Todofichajes – in Spanish)

Arsenal za ta iya fuskantar hamayya daga Chelsea da Bayern Munich da kuma PSG kan dan wasan Juventus Dusan Vlahovic mai shekara 22. (Il Bianconero – in Italian)
Manchester United ta gaza a yunkurin sayen dan wasan tsakiyar Italiya Manuel Locatelli, mai shekara 24, daga Juventus a bazara. (Sport Mediaset – in Italian)

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments