ASUU na neman kawowa Jam’iyyar Apc tarnaki a zaben 2023.
Daga Walid Hari
Shugaban ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa ASUU Emmanuel Osodoke yayi wasu kalamai dake neman ‘yan Najeriya su kaucewa zaɓen jam’iyyar APC mai mulki matuƙar ta gaza kawo karshen yajin aikin da ASUU ke yi tsawon watanni bakwai.
Waɗannan kalamai dai sun fusata ministan ƙwadago na tarayya Chriss Ngige inda ya fice daga taron neman mafita da shugaban majalisar wakilai ta tarayya Femi Gbajabiamila ya jagoranta don neman bakin zare tare da kawo karshen yajin aikin da kungiyar ASUU.
Menene ra’ayinku game da wannan kalamai?
Ya kuke ganin fusatar da ministan yayi game da kalaman?
Me kuke ganin ya dace a fi mayar da hankali a kansa game da yajin aikin na ASUU?