Yadda al’ummar garuruwan Nassarawa da Sabon Garin Tirkaniya suka tsinci kansu bayan kakaba musu dokar ta baci na kwanaki biyu

Al’ummar garin Sabon Garin Nassarawa dana Sabon Garin Tirkaniya Duk A Karamar Hukumar Chikun Dake Jihar Kaduna na cigaba da zaman kulle da gwamnatin jihar Kaduna da kafa musu sakamako wata hatsaniya data barke a tsakanin matasa yanke biyu a jiya lahadi bayan an shan ruwa wanda akafisani da  ‘Yandaba

Tun da fari kauyukan biyu akwai rashin jituwa a tsakanin matasan su Inda a sanadiyar hakan hargitsi ya barke wanda ya yi sanadiyar mutuwa matasa biyu aka kuma  jikkata wasu guda shida.

Bayan faruwar lamarin gwamnatin jihar Kaduna tuni ta tura tawagarta Jami’in tsaro domin kwantar da rikicin da ya barke a kauyukan.

A jawabin sa kwamashinan Al’amuran Tsaron Cikin Gida Mista Samuel Arowan yace Gwamnan Nasiru El’rufa’i ya bada umarin hana fita awa arba’in da biyar 45 daga yau litini

A ziyarar gani da ido da Jaridar Aksam Media takai tanar da ana zaman makoki mutuwan mutum biyu duk a Unguwar Sabon Garin Nassarawa duk da wacccen dokar sai dai babu al’ummomi a wajan.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments