Daga Hassan Umar Gwammaja
Kotun Shari’a Musulunci Dake Zamanta A Rigasa a Jihar Kaduna
Wacce Mai Shari’a Malam Anas Khalifa yake alkalanci tafara sauraron kara da kwamashinan ‘ Yansanda Jihar Kaduna ya Shigar yana karar Awaisu Jibrin Mai kimanin shekarau 35 mazaunin Tudunwada wanda yace shi Manomine
Bisa ga zarginsa da laifin zama da mata biyar a matsayin matansa na aure
Matan sune:
*Adama
*Sa’adatu
*Shafa’atu
*Fatima
Sai kuma ta biyar din mai suna
*Naja’atu wace aka auro a garinsu dake Karamar Hukumar Bichi a Jihar Kano
Tun ana saura mako guda ne a shiga watan Azumi na 1444AH
Awaisu ya ne mi auren Naja’atu a garunsu dake karamar hukumar Bichi, har take akasamu aminchiwar juna aka daura aure akan sadakin naira 40,000 tare da waliyinta da kuma wakil ango Awaisu a Garin Rigasar Jihar Kaduna
Saboda kar a wahar da su dangin amaryar basai anje gidansu amaryar ba
A ranar hudu ga watan Afrilun wannan shekarane Sarkin Dankandai Alhaji Audu Adamu ya kai karar Awaisu Jibrin Ofishin ‘Yansanda dake Rigasa a Karamar Hukumar Chikun cikin garin Kaduna bisa tsayawa Awaisu a matsayin wakil akan aura masa Naja’atu,
Yace bayan ya yi tsayin daka an daura wannan aure ba tare da bincike sai daga baya ya gano shi Awaisu ya saki matar sa ta mai sunan Fatima wato matarsa ta hudu,
Sai aka gano bai saki matar sa mai sunan Fatima ba
Shi yasa na zo wannan Ofishin,
Daga bisane Alkale Malam Anas Khalifa ya tambaye wanda ake kara kukaji kara? yace yaji, kafa yimta? yace ya fahinta, hakane yace ba haka bane,
Sai Mai Shari’a Malam Anas Khalifa yace ya ya ne?
Wanda ake kara yace shifa ton wata daya baya ya saki matatsa ta hudu Fatima, don haka kafin ya aure Naja’atu matansa uku,
Alkali ya tambaye shi ko kana da shida cewar kasaki Fatima yace bai bata takardaba amma ya ga yamata, sannan ya gawa Yayansa amma yace kar yasakita,
Ko ya gayamiki tace A’a
Kotu tambaye matar Awaisu ta farko ko tasan raguwa matan uku? tace tasansu, suma an tambaye su sunsan ita Uwar Gidan suka ce sun santa
Itan matar Awaisu ta biyar an tambayeta ko tasan wadacen matan na Awaisu guda hudu? Tace bata sansu ba, yasake tambayar suma matan gudu na Awaisu konsanta sukace ba su santaba,
Daga karshene Alkali Malam Anas Khalifa ya bada umarni akai wada ake kara Gidan Gyaran Hali zuwa ranar 12 ga watan Afrilun wannan shekarar
Mazaunin Gadan Gayan a Karamar Hukumar Igabi