Kungiyar matuka motocin Akorikura ta kasa reshen jihar kano dake railway, tana ci gaba da kokawa dangane da rashin guri na din din din da kungiyar take fama da shi duk da kudaden haraji da take Tarawa Gwamnati.
Shugaban kungiyar Abubakar Daniya Bala ne ya bayyana haka a lokacin da yake yiwa manema labarai Karin haske a ofishinsa dake birnin kano.
Shugaban yace ,kungiyar tana fuskantar kalubale saboda rashin wuraren tsayawa,Wanda ta sanya kungiyar tana kashe makudan kudade na haya Wanda da Gwamnatin ta Samar da guraren,ita ce za ta amfana da irin wadan nan kudade.
Abubakar yace,yana fatan wannan sabuwar Gwamnati da za ta karbi ragamar mulki za ta kalli fannin harkokin sufuri domin kawo masa daukin gaggawa da zai tallafawa matuka motocin Akorikura da sauran bangaren sufuri.
Shugaban ya kara da cewa,Gwamnatin da za ta karbi mulki,kamata yayi ta Samar da motocin sufuri, ta hanyar baiwa kungiyoyin sufurin da suka San bangaren domin baiwa ya’y’anta ,kasancewar kungiyar ta San irin wadanda za,a baiwa matsayin tallafawa rayuwarsu da Samar musu da ayyukan yi domin dogaro da kai.
Shugaban ya jaddada cewa, babu wani tagomashi ko tallafi da Gwamnati ta yiwa kungiyar duk da gudunmawar da suke baiwa Gwamnatoci a matakai daban daban, inda kuma, kungiyar Akorikura ta kasa reshen jihar kano dake railway, take taya zababben Gwamanan kano murna Dr.kabir Yusuf, bisa nasarar daya samu na zama Gwamnan kano.
Abubakar Daniya Bala, ya shawarci yankungiyar da su kasance masu bin dokokin da Gwamnati ta sanya musamman wajen mallakar takardun mota da Dorawa mota kayan da suka wuce kima da gudun wuce sa,a da karya dokokin da suka shafi kan hanya.
Ya kuma,bukaci yankungiyarsa da su ci gaba da baiwa shugabanci hadin kai da goyan baya domin samun damar bijiro da managartan shirye shirye da su inganta rayuwar alumma.
COV.
Ibrahim sani gama pyramid