Yadda aka ceto mutane 70 daga cikin 95 da aka yi garkuwa da su a Zamfara

A daren Juma’a da ya gabata ne iyayen yara a garin Wanzamai na karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara suka karbo kimanin yara 70 daga cikin mutum 95 da ‘yan bindiga suka sace makwanni uku da suka gabata.

Mutanen da aka karbo sun hada da maza da mata wadanda akasarinsu matasa ne masu shekaru kasa da 20 da yara ‘yan kasa da shekara 10 da kuma dattawa hudu.

Tun bayan sace mutanen ne al’ummar garin na Wanzamai suka fara neman hanyar da za su bi wajen ceto mutanen nasu.

Daya daga cikin mutanen garin da ya bukaci BBC ta sakaya sunansa ya ce wadanda aka sako sun kanjame sun koma kamar kwarangwal.

Ya kara da cewa Allah ne Ya karbi addu’o’insu saboda akwai gidaje da aka daukar wa mutane hudu har zuwa goma.

Mutumin ya kuma nuna farin ciki inda ya ce karbo mutanen ya faranta wa dukkan ‘yan garin rai.

Shi ma daya daga cikin iyayen yaran da aka karbo wanda BBC ta boye sunansa ya ce sai da suka biya kudade kafun aka ba su ‘ya’yan nasu.

“Sai da wasunmu suka sayar da gidajensu, wasu kuma gonaki sannan wasu kuwa sai da aka yi bara aka tara kudi aka kai wa ‘yan bindigar kafun suka sako su” in ji shi.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments