Wata mata ta sha da kyar bayan da wani magidanci fada su da Sara har cikin daki

Rundunar ƴan sandan a yankin Ashanti da ke Ghana ta ce ta fara bincike kan wani lamari da ya faru, inda ake zargin wani mai gida da sassari wani ɗan haya da ƴaƴansa biyu.

Sanadiyyar faruwar lamarin ne ɗaya daga cikin yaran ɗan ƙasa da shekara biyu ya rasa ransa.

Yanzu haka ɗan hayan da ƴarsa mai shekara 17 suna kwance a babban asibitin Ashanti cikin mummunan hali sakamakon raunuka da suka samu sanadiyyar sarar.

Tuni dai jami`an ƴan sanda suka ce sun kama wanda ake zargi kuma tuni suka fara bincike kan lamarin

Wannan lamari na ranar Juma`a ya faru ne bayan wata sa-in-sa tsakanin ɗan mai gida da wasu ƴan haya, bayan zargin ɗan mai gidan ya hana su shiga ɗaki, saboda a cewar sa kuɗin hayarsu ya ƙare.

Bayanai sun ce matar ɗan hayan da aka sara ta sha da ƙyar.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments