Qungiyar Inuwar masarautun kano 5 ta Wakilci zama na musamman a Tahir Guest Palace dake Nassarawa GRA, tare da Kungiyar N G O ta Perl. Org. Project, da kuma kungiyar Hasken Kano,domin zakulo muhimman Ayyukan ci gaba ga wadannan masarautu namu masu Albarka Suke Buqata.
Tun farko kungiyar NGO ta Perl. Org. Project, ta fara Ganawa da wakilan sarakunan mu Na masarautun mu Guda biyar,inda daga ko waacce masarauta aka wakilci kamar haka:
* Masarautar Kano, Mai Girma Fagacin Kano.
* Masarautar Bichi, Mai Girma Falakin Bichi.
* Masarautar Rano, Mai Girma Matawallen Rano.
*Masarautar Gaya, Mai Girma Makaman Gaya Hakimin Albasu.
* Masarautar Karaye, Mai Girma Ciroman Karaye.
Hakika burin wannan kungiyoyi da Masarautun mu shi ne nunawa al’umma hanyar data dace domin kawo Gyara, da ci gaban Al ummar masarautun Namu.
Saboda haka Ake kira da Yan Qungiyoyi da jama a yan garuwan da suke qarqashin masarautar kano dasu Bincuko aiyuka da matsalolin da jama ar wannan yanki suke fama dasu kuma suke Buqata..
Abubuwan da ake Buqata sun hada da
(1) RUWAN SHA
(2). ILIMI
(3). NOMA..
(4). HANYOYI
(5). LAFIYA
(6). AYYUKAN
(7). MAHALLI
(8). WALWALAR
Da kuma sauran matsaloli da Buqatun al umma da bamu ambace suba..
Dan haka ake kira da yan wadanna. Yanki da su turo wannan Buqatu da kuma matsalolin Al umma da kuma sunan inda suke buqatar ai wannan ayyuka ko kuma hotunan Wuraren Kuma su zama Wakilai na Zaman da za ai tareda Qungiyoyin Cigaban Al umma qarqashin Jagorancin Iyayen qasa Hakimai da dagatai da masu Unguwan ni Na wannan Yankuna Domin hada wannan kundi da kuma gabatar da wannan aiki ga mai martaba sarki kamar yadda ya bada dama ayi..
Domin Neman qarin bayani ko Turo bayanan da aka samu sai atuntubi wannan Numbobi 09138959130
07032036398
08107064022