Matashin mai suna Geng Quanrong ya kashe wata budurwa mai suna Ummukulsum Sani ta hanyar caccaka mata wuka.
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce, lamarin ya faru ne a unguwar Dorayi Babba da ke jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce, matashin mai shekaru 47 ya haura har gidan su yarinyar inda ya kashe ta har lahira.
Ɗan Chinan dai na zargin Ummukulsum da yaudararsa, ta hanyar ƙin aurensa bayan ya daɗe yana yi mata hidima.
Hakan ce ta sa ransa ya ɓaci, ya kuma je har gidansu dake unguwar Yamadawa a Dorayi Babba ya haura cikin gidan don aiwatar da mummunar nufin sa.
Bayan da ya haura ne ya shiga ɗakin yarinyar ta taga, ya zaro wuka ya fara caccaka mata a wuya da kafaɗunta.
Chaka mata wuƙar ke da wuya mahaifyarta ta yi ihun neman taimako, inda wani matashi ya yi kukan kura domin ceton su.
A cewar Kiyawa bayan samun labarin ne kwamishinan ƴan sandan Kano ya tura jami’ansa karkashin DPO na Dorayi Babba CP Abubakar Lawan.