Hukumomi a Tunisiya sun ce sun gano gawawwakiin wasu ƴan-cirani 14 a tekun ƙasar.
An ruwaito cewa ƴan-ciranin sun fito ne daga ƙasashen hamadar sahara, inda suke kokarin tsallakawa zuwa Italiya.
Sai dai ba a bayyana cewa ko ƴan-ciranin 14 na cikin jirgin ɗaya ko kuma daban-daban a yayin tafiyar tasu.
Tunisia dai ta zamo hanyar da ɗaruruwan ƴan-cirani ke bi domin tsallakawa zuwa Turai, inda alkaluman Majalisar Ɗinkin Duniya suka nuna cewa ƴan-cirani 12,000 da suka isa Italiya a wannan shekara sun bi ta Tunisiya.