Likitoti sun bukaci shugaba Buhari ya kara mako guda a London domin duba lafiyar sa

Buhari na daga cikin shugabannin kasashen duniya da suka halarci bikin nadin sarautar Sarki Charles III da aka yi a London a ranar Asabar da ta gabata.

Shugaban  zai tsawaita zamansa a London da mako guda, in ji kakakin fadar sa Femi Adesina.

Wata sanarwa dauke da sa hannun Adesina ta ce likitan hakori da ke duba shugaban ne ya ba da shawara kan ya tsawaita zaman nasa a London domin a yi masa aiki.

“Kwararren likitan ya bukaci ya ga Buhari cikin kwanaki biyar domin wani aiki da aka riga aka fara yi masa.” Sanarwar ta Adesina wacce VOA ta samu kwafi ta ce.

A ranar 29 ga wannan wata na Mayu, Buhari zai kammala wa’adin mulkinsa na biyu.

Zai mika shugabancin kasar ga Bola Ahmed Tinubu da ya lashe zaben da aka yi a watan Fabrairun da ya gabata.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments