Rahotanni na nuni da cewa wasu mutane uku sun shiga hanun jamian rundunar yan sanda ta kasa bisa zargin su da sakin baki akan uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari.
Wadanda ake zargin an kama sun hada da Salisu Isyaku, Salisu Habib da Zubairu Ahmed.
Majiya mai tushe daga jamian tsaro tace an Kama wadanda ake zargin ne tun a shekarar da ta gabata ranar 14/12/2022
Majiyar ta kara da cewa anyi amfani da sashin fikra ne wajan gano wadannan mutane da suka yi sakin baki ga uwargidan shugaban kasa.