Hukumar zaba mai zaman kanta ta kasa ta karbi kason karshe na na’urar kada kuri’a da tantance masu zabe wadda ake kira da BVAS.
Wata sanarwar da kwamashinan hukumar mai lura da wayar da kan masu zabe Mr Festus Okoye ya rabawa manema labarai ya yi bayanin cewa, shugaban hukumar Farfessa Mahmud Yakubu tare da wasu manyan jami’an hukumar ne suka karbi kayan a babban filin jirgin sama na kasa da kasa dake birnin Abuja .
Okoye ya ce hukumar ta kebe manyan filayen jiragen sama 4 da za su kasance cibiyoyin da za a yi amfani da su wajen rarraba na’urorin zuwa sassan kasar nan
Filaye da aka kebe sun hada da babban filin jirgin sama na Kano da Legos da Abuja da kuma Fatakwal.
Kimanin watanni 4 ke nan jiragen sama ke ta sintirin raba na’urorin BVAS zuwa jihohi a dai dai lokacin da ya rage kasa da kwanaki 50 a gudanar da babban zabe a kasar.