Rundunar ‘yan sanda ta kasa reshen jihar Imo ta kama wasu ake zargin ‘yan haramtacciyar kungiyar fafutukar kafa kasar Biafra ta IPOB su tara.
A sanarwar da kakakin rundunar Henry Okoye ya fitar, ‘yan sandan sun ce sun kama daya daga cikin jagororin mutanen mai shekara 48 ne a maboyarsa a Umuahia babban birnin jihar ta Abia.
Okoye ya ce kwamishinan rundunar ce ya bayar da umarnin kama mutumin domin ya bayyana sauran wadanda suka aikata kisan.
Sanarwar ta kara da cewa mutumin da ake zargin ya tabbatar wa ‘yan sanda cewa shi ne kwamandan ‘yan IPOB a yankin Mbaise a jihar.
Sauran mutane uku da aka kama din duk ‘yan yankin Mbaise ne kuma an kama su da hujjoji da ke nuna cewa su ne suka aikata kisan in ji rundunar ‘yan sandan.
Jami’an tsaro sun kama jagoran a-ware na Biafra a Finland
Kwamishinan rundunar ‘yan sanda na Imo Ahmed Barde ya yaba wa jami’an nasa bisa kokari da suka yi wajen kama mutanen da suka kashe ‘yan sandan.
Ya kuma bukaci al’umma ta bai wa ‘yan sanda hadin kai wajen gano maboyar bata-gari a duk inda suke.
Gwamnatin Najeriya dai ta ayyana kungiyar IPOB a matsayin haramtacciya tare da gargadin ‘yan kasar kar su shige ta.