Jami’ar Yusuf maitama Sule,ta sha alwashin kara bunkasa harkokin ilimin fassara da tafinta da sauran abubuwan da suka shafi furta yaren Hausa domin habaka fassara ga masu tasowa.
Shugaban kula da sashin yare na jami’ar farfesa Ayuba shehu Ahmed Rufai,ya bayyana haka a lokacin bude taron karawa juna sani na kwanaki uku akan fassara da tafinta,Wanda ake gudanarwa a jamiar dake nan jihar kano.
Shugaban yace, makasudun gudanar da taron domin a kara bunkasa fahimtar masu fassara da suka danganci kafafen sadarwa da kotuna da asibitoci da makarantu da sauran bangarori daban daban na ilimi ake furta yare.
Ayuba shehu,ya jaddada cewa,shirya irin wannan taruka zai taimaka gaya wajen wayar da kan alumma da bunkasa harkokin fassara da tafinta da sauran abubuwan da suke wahalar da masu fassara.
Ya kuma yabawa shugaban jami’ar Farfasa mukutar Atiku kurawa,bisa gudunmawar da yake bayarwa wajen ci gaban harkokin ilimi na Jami’ar, musamman sashin yare.
A jawabinsa Shugaban masu fassara ta Kasa,Farfesa Hafizu Miko Yakasai, yace,fassara na daga cikin bangarori na rayuwa daban daban, inda fassara tana taka muhimmiyar rawa wajen bunkasar yare ya zama daukakakke a koina a fadin Duniya.
A don haka yake kira ga Gwamnatin kasar nan da sauran masu zuwa da tsaki kan su baiwa kungiyar masu fassara da cibiyar kula da harkokin fassara, da su baiwa fassara da tafinta da yare kulawar da ta kamata domin bunkasa harkokin yare,musamman na Hausa.
Farfesa miko,ya bukaci kungiyoyin da fannin Gwamnati da suka shafi na sadarwa da sharia da makarantu da su shigo fannin harkokin fassara a dama da su,domin kara samun ilimi.
Shima a jawabinsa injiniya mustafa Habu ringim,Wanda shine shugaban ingausa global,ya nuna mutukar farin cikinsa bisa lambar girmamawa da jami’ar Yusuf Maitama Sule ta bashi,sakamakon gudunmawar da yake bayarwa wajen ci gaba harkar fassara da tafinta da yaren Hausa a fadin kasar nan.
Daga karshe yayi kira ga kafafen sadarwa da sharia da makarantu da dai sauran masu fassara da su mayarda hankali wajen koyan fassara yadda yakamata.
Ibrahim sani gama pyramid.