Matasa sun gudanar da zanga-zangar lumana ne Dan nuna rashin Jin dadinsu bisa yadda mahukunta da jami’an Hisba Dana karota ke uzzura musu a kasuwar da tashar motar
Salisu yahya Umar guda ne daga cikin shuwagabanin masu aiki a kasuwar bangaran tashar mota ya bayyana mana ceawar matsalar tashar motar ta samo asaline tun lokacin da Gwamnatin da ta shude ta tashi tashar motar daga new-road Sabon- gari tasa suka dawo by-pass hanyar hotoro
Salisu ya ce bayan sun dawo sabon gurin ne aka bijiro musu da wasu sabbin tsare-tsare na karbar kudade a matsa haraji
Ya Kara da cewa matasan dake kasuwar kan Yi Wani Abu da ake cewa KAYI-NAYI Amma sai suka wayi gari wasu daga jami’an tsaro sun shiga wannan harkar Wanda Hakan yasa matasan suka fusata
Wakilin Aksammedia na fadar Gwamnatin jihar Kano Adamu Dabo ya bayyana mana cewar jami’an Hisba Dana karota dake tashar motar sun Kai Kara ga jami’an ‘yansanda Suma kungiyar ma’aikatan tashar motar sun ce za su ci gaba da bibiyar lamarin