An Haifeshi 20/8/1951,
Yazama Shugaban Qasa 30/6/2012,
Anyi Masa Juyin Mulki 3/7/2013,
Ya Rasu A Prison 17/6/2019.
Shaheed Mursi Rahimahullah
Tarihin Musulunci Na Wannan Qarnin Bazai Manta Da shiba Har Abada.
Allah Ya Jadada Rahama Gareshi Yasa Aljarnar Firdausi ce Makomarsa.
Daga A S Gwammaja
Shine Shugaban Qasar Da Yaje Majalisar ‘Dinkin Duniya Agaban Yahudawa Yabaiwa Annabi (S.A.W) Kariya.
Shine Shugaban Qasa Na Farko Acikin Shugabannin Qasar Egypt Da Yaja Sallah A Masallacin Annabi (S.A.W) Madina,
Shine Shugaban Qasar Da Ya Bud’ewa Falatsinawa Iyakar Qasar Egypt Domin Zalincin Da Yahudawa Keyi Musu,
Shine Shugaban Qasar Da A Lokacinsa Malamin Addini, Hafizin Qur’ani, Kuma Qwararran Engr A Fannin Boko,
Shine Shugaban Qasar Da Yafito Da Malamai Da Duk Wanda Aka ‘Daure Bisa Zalinci A Mulkin Husnul Mubarak,
Shine Yayi Qoqarin Tsarin Qasar Egypt Ya Tafi Daidai Da Tsarin Musulunci,
Shine Wanda Larabawa Masu Qawance Da America Suka Had’a Baki Da Isra’el Wajen Kifar Da Gwamnatinsa,
Shine Shugaban Qasar Da Yayi Shahada A Prison A Hannun Maqiya Addinin Allah,
Shine Shugaban Qasar Da Aka Hana Y’an Uwansa, Da Masoyansa Su Sallaci Gawarsa.