Mutumin mai suna Hamisu Garba Gunduwawa ya tsallake rijiyar da baya a yayin da wani matashi mai suna Aminu Sani Dan asalin Jihar Jigawa karamar hukumar Garki yayi kokarin kwace masa mashin mai kirar Boxer
A cewar Hamisu, matashin bara won yayi kokarin maka masa tabarya ne inda Allah bai taimaka shi ba sai suka kama kokawa daga bisani ya hada da ihu barawo sai jama’a suka kai masa dauki
Bayan da barawo ya ji jama’a zasu hallara saucy yayi kokarin tserewa kana jamian vigilant suka bishi suka yi ram da shi
A cewar kwamandan vigilant “Yayi yunkurin kwatar babur boxer ja a hannun Hamisu Garba Gunduwawa
Lokacinda ya daukeshi acaba zuwa tammawa yayi Masa karyar cewar Wai foundation zasu haka
Shine ya kudundune wannan itacen yace Wai digace
Mun turashi zuwa Gezawa Police station Abin ya faru 10:04 na safe
Yayi yunkurin buga Masa wannan itacen Sai Saida sukayi kokawa shine barawon ya gudu Sai vigilante suka bishi bayan anyi ihu Allah yasa aka kamashi saboda baisan Cikin unguwaba”