Wani manomi a kasar Uganda mai suna Musa Hashya da ya auri mata 12 ya bayyana cewa yanzu baya adawa da matansa na amfani da maganin hana haihuwa domin hana ci gaban iyalinsa.
A cewar jaridar Daily Star ta Burtaniya, Hasahya, yana jin radadin tsadar rayuwa a kauyen su na Bugi said, a Uganda, inda yake zaune tare da iyalansa.
Hasahya, mai shekaru 67, ta ce, “Ba zan iya jurewa haihuwa ba saboda karancin kayan aiki. Kuma a kan haka na shawarci duk matana da suka kai shekarun haihuwa da su fara amfani da tsarin iyali.
Ina kuma ba masu sha’awar auren mata sama da hudu kwarin gwiwa da kada su yi hakan domin abubuwan akwai hadari ba su da kyau”.
Ya kara da cewa, “Kudaden da nake samu ya ragu sosai a tsawon shekaru saboda tsadar rayuwa kuma iyalina sun kara girma”.
Musa, wanda kuma yana da jikoki 568, yana zaune ne a wani katafaren gida mai daki 12. Ya auri matarsa ta farko Hanifa a shekarar 1971 yana dan shekara 16.
Ya ce duk da yake yana iya raba ‘ya’yansa da jikokinsa, amma bai san su duka da sunan su ba.