Ikechukwu Samuel, babban limamin cocin Shiloh Word Chapel da ke Abuja ya shawarci Peter Obi da ya koma ga matakansa da ya biyo a sakamakon zaben 2023
A sanarwar da ya fitar, ya buga misali da yadda Israilawa suka zabi Saul a matsayin sarki a madadin zabin da Allah ya yi musu na Annabi Isma’il, kamar yadda yazo a Injila
Malamin ya ce ya yi mamakin yadda Obi da ya yi takara a jam’iyyar Labour yake mamakin yadda yake fama da kwace hakkinsa a madadin ya waiwaya baya
Ina ba Peter Obi kwarin gwiwar ya daidaita da dukkan malaman addinin Kirista da fastoci a Najeriya, duk wanda ya shawarce shi da ya ki bin ta malaman coci to shi ya kada shi.
” Sai baka nan za a yi kewarka, ga misalin T.B Joshua, inji fasto Malamin ya kuma bayyana yadda fasyyo T.B Joshua ya sha fama da mutane a lokacin da yake raye, amma ya samu karbuwa bayan mutuwarsa.
A tun farko, Peter Obi da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar basu amince cewa Bola Ahmad Tinubu ne ya lashe zaben da aka yi a bana ba.