Tsohon shugaban kasar Najeriya na tunanin cewa, ya kamata ‘yan Najeriya su yi rayuwa yadda ya kamata ake kallon kasar a matsayin uwa a Afrika
Baban Iyabo, kamar yadda ake kiransa ya ce ‘yan Najeriya a zamaninsa sun iya yanke shawari mai kyau wajen zaban shugananni
Kana Ya bukaci ‘yan Najeriya da su rungumi hadin kai, wanda yace shi ne kadai maganin duk wata matsala a kasar nan
Ya bayyana hakan ne a wurin bikin ba da lambar yabo ta National Daily Awards da aka gudanar a yau Juma’a 12 ga watan Mayu a jihar Legas.
Obasanjo ya kuma bayyana cewa, a zamaninsa an ga gogaggun ‘yan siyasa da ke fafutukar samar da shugabannin da suka dace.
A bayaninsa, Obasanjo ya ce, daga abin da ya koya a aikinsa na kwantar da tarzoma da wanzar da zaman lafiya shine, kasar da ke zaune lafiya, cikin aminci ce ke iya ci gaba
Ya kuma bayyana cewa, yana da kyau kowacce kasa ta mai da hankali ga adalci, daidaito da kuma mutunta juna, rahoton Punch.
‘Yan Najeriya na daban ne, inji Obasanjo Daga nan, ya siffanta ‘yan Najeriya da wasu kalan mutane na daban da ke iya cimma komai suka tunkara a duniya.
Sai dai, ya yi kira ga a gyara abu daya da ke damun mutane da yawa, inda yace kowa ya rungumi hadin kai da taimakon kasar ta ci gaba yadda ya kamata.