Wani Dan kasar Jamus ya shaki yanci bayan kwashe shekaru a tsare

Bayan shafe fiye da shekaru hudu ana tsare da shi a yankin Sahel, masu garkuwa da wani dan kasar Jamus sun sako shi.Mutumen mai shekaru 63 mai suna Jörg Lange,kungiya mai zaman kanta da yake aiki da ita, Help, ta tabbatar da sako shi daga hannun yan taadda

Manajan darakta na kungiyar ta Help, Bianca Kaltschmitt ya rubuta a cikin wata sanarwa da aka mikawa manema labarai a Jamus cewa, “Mun sami kwanciyar hankali sosai kuma muna godiya cewa abokin aikinmu Jörg Lange, bayan fiye da shekaru hudu da rabi, ya koma ga danginsa.”

Gwamnatin Jamus ba ta bayar da karin haske dangane da hanyoyin da aka bi wajen ganin an sallami Jorg Lange, yan lokuta da sallamar sa,an saka shi jirgi inda ya kama hanya zuwa Jamus.

An yi garkuwa da Jörg Lange ne a ranar 11 ga Afrilu 2018 a yammacin jamhuriyar Nijar.

An bayyana cewa wasu mutane dauke da makamai akan babura kusa da yankin Ayoru, da ke kan iyaka da kasar Mali mai fama da hare-haren mayakan  masu ikirarin jihadi suka yi awon gaba da shi. An sako direbansa dan Najeriya jim kadan bayan haka.

Sai dai a cewar  jaridun kasar  Jamus, masu garkuwa da shi sun sayar da Jörg Lange bayan sace shi ga kungiyar masu ikirarin jihadi “Daular Islama a cikin Sahara” (EIGS).

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments