Daga Musa Mudi Dawakin Tofa.
A jiya asabar 10/12/2022, aka gabatar da taron rufe bita (Daura, a larabce) da Gidauniyar yada ilimin Addinin Musulunci da Wayar da Kan Alumma mai suna “Bin Baaz Islamic Foundation for Propagation and Counseling” BBIFPC ta gabatar ga matan aure da matan da aka sanyawa ranar aure a cikin Masallacin Makka dake garin Dawanau a jihar Kano.
An dai gudanar da Daurar ne tun a ranekun 26 da 27 ga watan Nuwamba na shekara ta 2022 da manufar inganta rayuwar aure a mahangar addinin Musulunci wanda manyan malaman Addinin Musulunci daga ciki da wajen jihar Kano suka gabatar da batutuwa daban-daban.
A yayin taron rufewar, mata 226 ne suka rabauta da shaidar halartar Daurar (Seminar Certificate of Attendance),
kana wasu daga cikin mahalarta da suka nuna halin kwazo da halaye nagari kamar: Mata goma na farko da suka fara halarta da wadanda suka amsa tambayoyi da wacce ta takaice duk batutuwan da malamai suka gabatar cikin kwanaki biyu, duk sun rabauta da kyautar littafi mai suna “Zararren Takobi Kan Bidi’oin Watannin Shekara” wallafar Jagoran gidauniyar BBIFPC a jihar Kano Sheik Abdulwahhab Abdallah.
Kazalika, suma ‘yankwati da wadanda suka tallafa tun daga farko har zuwa ranar rufe Daurar sun rabauta da shaidar yabo da godiya (Certificate of Appreciation) inji Sheik Auwal Bin Umar Dawakin Tofa Jami’i mai kula da gidauniyar Bin Baaz….. A Kano ta Arewa.
Dr Nasidi Uba Kura na daya daga jagororin gidauniyar Bin Baaz…A Kano kuma daya daga cikin ‘yankwamatin da suka shirya Daurar a garin Dawanau ya ce “na daga cikin manufar gidauniyarsu kula da matsalolin dake damun al’umma wanda aure ginshiki ne kuma yana na daga cikin al’amuran da suke fuskantar tarin matsaloli a wannan zamani, a don haka suke kokarin tara al’umma musamman ma’aurata da ma masu niyyar yin auren, don su kara wayar da su, sanin matsalolin aure da kuma yadda za a magancesu, tun kafin su faru.
Fatima Ahmad Adam Bandirawo da Nabila Abdullahi da kuma Maryam Muhammad Karaye na daga cikin mahalarta da suka bayyana godiya da gamsuwarsu da shirin Daurar.
Uba kuma Maigirma Dagacin Dawanau malam Muktar Sa’idu da malam Adamu Abdu da malam Faruk Haruna da malam Ahmad Yahaya da malam Ali Dawanau da malam Sulaiman Abdul Danguguwa na daga cikin wadanda suka shaida taron rufe Daurar a garin Dawanau yankin karamar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano dake kasar Nigeria.