Umma Getso, ta fadi fa’idodin zabar jam’iyar APC a zabukan dake tafe

*zaben Tinubu alheri ne ga ‘yan Nigeria @Umma Getso*

tsohuwar ‘yar takarar mataimakiyar Shugaban kasa a jam’iyyar YPP Hajiya Umma Getso ta bayyana cewa zabin Dan Takarar Shugaban kasa na jam’iyyar APC Asiwaju Ahamad Bola Tinubu zai zamewa ‘yan Najeriya alheri da samun Mafita.

Hajiya Umma Getso ta bayyana haka ne a yayin tattaunawa da manema labarai a ofishinta dake Abuja, tace duk wadanda ke neman Shugabancin kasar nan a zabe mai zuwa babu wanda ya fishi cancanta, la’akari da gogewarsa na sanin makamar aiki da habbaka tattalin arzikin kasa.

Ta kara da cewa idan aka kalli jihar Legas a yadda take kafin Tinubu ya zama Gwamna da kuma yadda ta koma a lokacin da ya zama Gwamna wannan wati babbar alama ce dake bayyana irin nagartar Dan Takarar, kazalika da irin gagarumar Gudummuwarsa aka kafa wannan Gwamnati ta shugaba buhari sai dai ta saba da wasu manufofin da aka gina tsarin wanda hakan yasa Tinibun yake fatan zama Shugaban kasar domin cika wadannan kyawawan manufofi ga yan Nigeria inji ta.

Umma Getso tace babu shakka an samu kura kurai a mulkin shugaba Buhari amma da zarar Tinubu ya zama Magajinsa za’a samu gagarumin gyara ta fuskoki daban daban,don haka kamata yayi a samu cikakken hadin kai ga ‘yan kasa Domin zabar Tinubu.

Bai kamata a samu wasu na nuna kabilanci akan rashin cancantar Tinubu ba,domin irin Hallacin da ya nuna a lokacin da ya goyi bayan shugaba Buhari a zaben 2015 har aka samu nasara,don haka yanzu lokaci ne da za’a mara mashi baya shima ya nuna irin nasa kwarewar a Shugabancin kasarnan.

Umma Getso tayi kira ga matasa da su guji siysar daba da jagaliya wanda hakan ke kai su ya baro, a maimakon hakan su jajurce su shiga siyasa ta tsabta domin suma a rinka damawa dasu a sha’anin kawo Cigaban kasa,

Umma Getso ta shawarci sauran al’ummar kasarnan da su bada cikakken hadin kai don gudanar da ingantaccen zabe cikin tsabta don dorewar dimukuradiyya a dungulalliyar kasarmu Nigeria.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments