Sifeta Janar na ‘yan sandan Najeriya, Alkali Usman Baba, ya bayyana gamsasshen dalilin da yasa hukumarsa bata kama tare da gurfanar da Bola Ahmed Tinubu ba
A cewar Alkali Baba, dukkan korafin da kungiyoyi masu zaman kansu suka shigar kan satifiket din bogin, zargi ne babu wani tabbaci shiyasa basu yi aiki da shi
Ya kara da sanar da cewa kotun koli ta taba yanke hukunci kan wannan karar a 2002 wacce Cif Gani Fawehinmi ya shigar, don haka ba zasu sake budo ta ba
IGP din yayi bayanin cewa Tinubu ba abun zargi bane ga ‘yan sandan Najeriya, Channels TV ta rahoto.
Dalilin da yasa ‘yan sandan basu farauci ‘dan takarar shugabancin kasan na APC ba yana cikin wata rantsuwar kotu da aka shigar a gaban babban kotun tarayya dake Abuja ta hannun wani lauya mai suna Wisdom Madaki.
A wata kara da wata kungiya mai zaman kanta ta shigar inda ta bukaci sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya da ya kama tare da gurfanar da Tinubu kan satifiket din bogi, IGP yace ‘yan sanda basu da karfin ikon gurfanar da Tinubu ba tare da cikakken bayanin laifin da yayi ba