Litinin din nan ne, sojojin kasar Sudan da jagororin fararen hula, suka sanya hannu kan wata yarjejeniyar siyasa, da za ta kawo karshen takaddamar siyasa da ma kafa gwamnatin rikon kwarya ta tsawon shekaru biyu.
Kwamandan sojojin kasar Abdel Fattah Al-Burhan, da Mohamed Hamdan Dagalo, kwamandan rundunonin kai daukin gaggawa ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar a madadin sojojin kasar.
A halin da ake ciki kuma, wakilan dakarun kawancen neman ‘yanci da canji, da jam’iyyar juyin juya hali, da sauran kungiyoyin siyasa, da ma’aikata, da na fararen hula, sun sanya hannu kan yarjejeniyar a madadin kungiyoyin siyasa