Mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR, CNOL, ya bukaci al’ummar jihar kano dasu bawa hukumar kidaya ta kasa hadin kai wajen ganin sun gudanar da aikin kidayar jama’a da za gudanar a wannan shekara.
Sarkin ya furta haka ne lokacin da yake karbar bakuncin shugaban hukumar kidaya ta kasa Alhaji Nasiru Isah yayin da ya ziyarce shi a fadarsa.
Alhaji Aminu Ado Bayero yace, aikin kidaya nada matukar mahimmanci a kasar nan tahaka ne hukuma za tasan adadin mutanen kasar nan.
Haka kuma Sarki Bayero ya godewa shugaban hukumar kidayar ta kasa Alhaji Nasir Isah Kwara da sauran yan tawagarsa.
Anasa jawabin shugaban hukumar kula da aikin kidayar ta kasa Alhaji Nasir Isah Kwara yace jihar kano tana daya daga cikin jahohin kasar nan da ake alfahari dasu a wajen yawan al’umma.
Sa Hannu.
Abubakar Balarabe Kofar Naisa Babban Sakataren Yada Labarai na Masarautar Kano.
5/12/2022