Shugabar makarantarGuidance standard Hajiya Bilkisu Suleiman tayi Kira ga iyaye dasu kasance masu tantance irin makarantun da zasu aike ya’ya yensu don gudun gurbacewar tarbiyyarsu.
Barista Bilkisu Sulaiman ta yi wannan kiran ne a ranar bikin yaye daliban makarantar da raba kyautuka da lambobin yabo karo na bakwai Wanda yayi dai dai da ranar matasa ta duniya Sha biyu ga watan agustan ko wace shekara 12_8_2023 in da suka raba kyautuka ga wasu fittattun mutane masu taimakawa a fannoni daban daban don cigaban al’umma har mutane ashirin(20) Barista tace sai iyaye sun kula da wace makarantar zasu Kai ya’yansu a fannonin karatun zamani dana addini baki daya.Guda daga cikin wadanda aka karrama da lambar yabo kuma wacce ta assasa gidauniyar Harken al’umma Mai taimakawa marayu Hajiya Aisha Aminu Ahhali ta bayyana sirrin ci gaban gidauniyar su da cewa tsarkake niyya shine kan gaba domin muddin mutum zaiyi aiki tukuru domin wani ya amfana to ba shakka zai samu taimakon Allah don haka tayi Kira ga sauran kungiyoyi dasu jajirce wajen yin abun da mutane zasu amfana domin hakan zai kaisu ga irin wannan matsayin ko ma Wanda ya fishi. Alhaji Bashir Abdurrauf sunusi ya yi jawabi a madadin iyaye yace makarantar Guidance standard ta shahara wajen bayar da tarbiyya dubo da yadda shugabar makarantar take bayar da gudummawa a ko wane fanni na al’umma ya kuma yaba mata don gane da hakan.wasu daliban da aka yaye Habib Sadi gabar,i Saddiq Bashir Muhd, da Fatima salisu Bala su gode da irin kwazon malamansu Wanda ya gadar da nasarar da suka samu a jarrabawarsu ta kammala karatunsu sun kuma godewa iyayensu tare da shan alwashin bawa mara,da kunya a karatunsu da zasu Dora andai gudanar da taronne a babban dakin taro na mahmud tukur dake tsohuwar jami’ar Bayero.