Shugabancin kungiyar matuka motocin haya ta kasa reshen malam Kato,ya yi Kira ga Gwamnatin jihar Kano da sauran mahukunta a fannin harkokin sufuri da su kawo musu dauki dangane da wa, adin da aka baiwa masu gudanar da Sana,oinsu a cikin tashar ta malam Kato su tashi batare da nema musu wani wurin Ba.
Shugaban matasan masu Sana, ar tukin motocin haya na tashar malam Bako shatima ne ya yi wannan kiran a zantawarsa da manema labarai a madadin kungiyar ta matuka motocin haya dake malam Kato a nan jihar Kano.
Yace kuginyar tana cikin wani mawuyacin hali da yakamata mahukunta da sarakuna da sauran masu ruwa da tsaki Su kawo yankungiyar da sauran alummar dake Sana, a cikin tashar dawajenta kasancewar wasu mutane suna ikirarin cewa Gwamnatin jihar Kano ce ta hannun Ma,aikatar kasa da safiyo ne suka bada umarnin duk mutanen dake cikin wannan Tasha su tashi.
mal.Bako,yace sun kwashe akalla shekaru Ashirin suna gudanar da kasuwacinsu a ciki, inda yace, kimanin alumma sama da miliyan daya ne ke cin abinci a wannan Tasha, wadanda suka Hadar da :Direbobi da kanikawa da masu saye da siyarwa da dai sauran alumma daban-daban.
- Daga wakilin mu Ibrahim sani gama
Shugaban ya kara da cewa :yanzu haka Gwamnati tana ikirarin Samar da ayyukan yi ga matasa, bai kamata ta tashe su ba, sakamakon basu da wuri da za su je domin ci gaba da gudanar da hakkokinsu, A Don haka ne, kungiyar matuka motocin hayar take rokon Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Dakta Abdullahi umar Ganguje khadimul Islam, da dubi wannan lamari domin an dakatar yunkurin tashin alumma daga cikin tashar, Saboda ta nanne suke samun abin da za su ciyar da iyalansu.
Kungiyar ta ce, Gwamnatin jihar Kano, tana da matukar rawar takawa wajen dakatar da wannan yunkurin tashin alumma dake cin abinci a wannan Tasha, inda yace, alummar dake Sana, a a tashar suna biyan karamar hukumar Fagge haraji kasancewar tana karkashin karamar hukumar, Sai kuma, harajin jiha Shima alumma suna biya iya kokarnsu,saboda da haka, kungiyar matuka motocin hayar take rokon Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi umar Ganguje khadimul Islam ya tallafawa masu duba da halin da alummar suke ciki musamman a wannan lokaci da muke ciki na matsin rayuwa.
Daga karshe Shugaban kungiyar yace kungiyar tana ragewa Gwamnatin jihar Kano da ta tarayya nauye-nauye ta fannoni da dama, musamman ta hanyar Samar da ayyukan yi ga matasa da saukaka harkokin sufuri da Al, amuran yau da kullum, ya kuma kara da cewa :kungiyarsu a shirye take wajen ci gaba da baiwa Gwamnatin jihar Kano wajen bunkasar harkokin sufuri da tattalin arzikin kasar nan.
Malam Bako, bukaci yayan kungiyar da su ci gaba da gudanar da addu,oin samun sauki da zaman lafiya mai dorewa .