Daga Walid Hari.
Ɗan wani mutumin kasar Amurka da aka tsare a Saudiyya ya shaida wa Manema labarai cewa an yanke wa mahaifinsa hukuncin zaman gidan kaso na tsawon shekara 16 saboda sakonnin Tuwitar da ya wallafa da ke sukar gwamnatin kasar.
An kama Sa’ad Ibrahim Almadi wanda ke da shaidar zama dan kasashe biyu wato Saudiyan da kuma Amurka ne a watan Nuwambar bara a lokacin da yake kan hanyarsa daga Riyadh zuwa Florida don ganin iyalansa.
Kotun ta Saudiyyar da ta yanke wa Sa’ad Ibrahim Almadi hukuncin na tuhumar da neman tayar da zaune tsaye a Saudiyya, da kuma mara baya da samar da kudi ga ayyukan ta’addanci.
Tun da farko kotun ta so ta yankewa Mr Almadi hukuncin zaman gidan yari na shekara 42.
Dan nasa da ke zaune a Amurka ya kasa samun damar magana da shi.
Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ce ba ta da wani aiki illa kare ‘yan kasarta da ke waje.
Daga karshe dan nasa ya ce baya son mahaifinsa ya mutu a gidan yari.