Kungiyar hada Hadar wayoyin hannu ta jihar kano reshen kasuwar farm center tace ta samu nasarori da dama wajen bunkasa kasuwanci da samar da tsaro da sauran abubuwa da dama tun daga fara shugabancin kungiyar zuwa yanzu.
Shugaban kungiyar Hassan Abubakar Abdullahi, wanda Jami, in hulda da jama’a na kasuwar jamilu Abubakar ya wakilta ya bayyana haka a lokacin da yake Karin haske ga manema labarai dangane da nasarorin da shugabancin kungiyar kasuwar ya samu tun daga lokacin da ya fara mulki zuwa yanzu wanda ya gudana anan kano.
Yace kungiyar ta kuma inganta ta tsaftar kasuwa a lungu da sako ta yadda alumma za su ji dadin aiwatar da alamuransu, wanda kwamishinan muhalli na jihar kano Dr. Kabiru Ibrahim getso, Har lambar girmamawa ya baiwa kungiyar, sakamakon kokarinta wajen tsaftar muhalli.
A jawabinsa Shugaban kula da harkokin tsaro da kula da shige da fice na alumma, Alh zurkifulu, ya bayyana cewar, a Fannin samar da tsaro da yake shugabanta yayi nasarar dakile masu shigowa da wayoyin sata da sauran kayayyaki da suka danganci wannan sana,a ta hada Hadar wayoyin hannu.
Kamar yadda kuke gani a wannan hotunan, kayayyaki ne da sashin lura da harkokin tsaro tare da hadin Kan jamian tsaro na kungiyar kasuwar suka samu nasarar cafkewa wanda wasu ma daga ciki Allah ya baiwa zakarunsu sa, a sun gudu sun bar kayan, wanda suka Hadar da tabar Wai Wai da sukudayi da wayoyin hannu da kudade, kuma yanzu haka kungiyar tana gudanar da bincike Akan lamarin.
Ofisa zurkifulu ya ba da tabbacin cewa ba za su gajiya ba, wajan kakkabe duk wasu batagari da za su rika shigowa kasuwar domin cutar alumma yankasuwa da ma baki da suke shigowa Don kasuwanci daga wasu gurare. Inda kuma, yace kungiyar ta sasanta rigingimu da dama tsakanin yankasuwa da kama barayi tare mikasu hannu jamian tsaro domin hukuntasu.
Zurkifulu ya yabawa abokanan aikinsa da sauran yankungiyar bisa gudunmawar da suke bayarwa wajen Inganta alamuran kasuwar kodayaushe.
Ibrahim sani gama pyramid radio.