Tsohon gwamnan babban bankin CBN, Muhammadu Sanusi II, ya fito ya yi magana game da jita-jitar cire rubutun Ajami daga takardun Naira. A wani bidiyo da Legit.ng Hausa ta ci karo da shi a shafinsa na Twitter, an ji Mai martaba Muhammadu Sanusi II yana karyata rade-radin da ke yawo.
Ganin har wasu malaman addini sun fara fashin-baki a kan lamarin alhali bai tabbata ba, Sanusi II ya yi kira ga malaman su daina aiki da jita-jita.
“Akwai maganganu da suke ta yawo a kan canza kudin Naira, na ji malamai dabam-dabam; wasu masu zafi a kan zargin za a cire Ajami daga Naira.”
Ina so in yi amfani da wannan dama, in tabbatarwa al’ummar Musulmi cewa babu gaskiya a cikin wannan maganar.
Khalifan na Tijjaniya ya tunawa al’umma koyarwar addinin Musulunci game da yin bincike idan wani ya kawo labari, kafin a dauki mataki saboda nadama.