An yabawa sanatan kano ta tsakiya kuma tsohon gwamnan jihar Kano Tenuwa biyu Malam Ibrahim Shekarau bisa nazari da hangen nesa da yayi a lokacin gwamnatin said har ya kawo mashin din Adaidaita sahu.
Yabon ya fitone daga kungiyar Direbobin Adaidaita sahu ta jihar Kano a taron da suka gudanar domin karrama Malam Shekarau.
Taron karramawar ya gudana be a jihar Asabar karkashin jagorancin shugaban kungiyar Direbobin Adaidaita sahu Malam Nura Sabiu Umar, inda kungiyar tasu ta mika shedar girmamawa ga sanatan Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau
Da yake Jawabin Godiva sanata Shekarau ya yaba da karramawar da kungiyar Direbobin Adaidaita sahun suka yi masa in yaja hankalin su da sukasance masu bin doka da oda.