Gwamnatin tarayya tana kashe tiriliyan daya da digo daya a wajan biyan albashin maaikatan ta 89.000 a Kowacce shekara.

Gwamnatin kasar nan  sun bukaci shugaba Buhari ya kara yawan harajin da talakawa ke biya, ciki har da sanya haraji a kan kowanne mutuum mai samun naira dubu 30 kowanne wata.

Jaridar Premium times da ake wallafawa a kasar ta bankado wannan shawara da gwamnonin suka gabatarwa shugaban kasa lokacin wani taro da suka gudanar da zummar lalubo hanyar samarwa gwamnati karin kudaden kashewa.

Shawarar gwamnonin ta kuma kunshi aiwatar da rahotan kwamitin Stephen Oronsaye wanda ya bukaci rufe wasu ma’aikatun gwamnati da basu da tasiri ko kuma wadanda ayyukan su ke cin karo da na wasu ma’aikatu.

Rahotanni sun ce gwamnatin tarayya Na da ma’aikata dubu 89 ne amma kuma tana kashe naira triliyan 4 da biliyan 100 wajen biyan su albashi da alawus alawus kowacce shekara daga cikin kasafin kudin naira triliyan 17 da ta ke yi a shekara.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments