Shugabancin kungiyar kasuwar masu siyar da Siminti na Kasa reshen jihar Kano dake railway, na ci gaba da kokawa sakamakon, lalacewar da titin da ya tashi Daga railway ya zagayo shataletalen A.A.Rano zuwa Audu Bako,Wanda aka ta,allaka lamarin da rashin magudanan Ruwa.
Sakataren kungiyar masu siyar da Siminti na reshen jihar Kano, Abdullahi Baffa Hotoro ne,ya yi wannan kiran a ci gaba da kiraye_kirayen da kungiyoyin da suke yankunan suke yiwa Gwamnatoci a matakai daban daban.
Yace,kungiyar ta yi iya kokarinta wajen ganin an gyara wannan hanya amma, sakamakon in dambu yayi yawa ba yajin mai,kamar yadda Sakataren kungiyar ya shaidawa yanjaridu,Abdullahi Baffa,yace,kungiyar ta kashe kudade da dama domin ganin an inganta hanyoyin, amma,hakarsu Bata cimma Ruwa ba.
Abdullahi Baffa Hotoro, yace kungiyar tana biyan Gwamnatin tarayya da ta jiha da karamar hukuma kudaden haraji kamar yadda aka shardantawa kungiyar masu siyar da Siminti ta railway.
Sakataren kungiyar ya kuma,koka da yadda hukumomin dake lura harkokin tuki suke yawan cin mutuncin direbobin tirela,musamman na yankasuwa dake zuwa kasuwar siyar da Siminti domin kawo simintin,inda yace, sakamakon haka da yawa direbobin basa son kawo kayayyaki zuwa jihar Kano, domin gudun cin zarafinsu da wasu Daga cikin jamian tsaro suke yiwa direbobin tirelar.
Haka zalika, ya bukaci Gwamnati da masu Ruwa da tsaki a fannonin gyara_gyaran titina na jihar Kano da ma,aikatar ayyuka da su taimakawa alummar wannan yankuna kasancewar titinan suna haifar da cinkoson Ababen hawa tun Daga titin shataletalen hanyar railway zuwa shataletalen titin Audu Bako, Wanda haka na kawa tsaiko ga alummar dake bin wadannan hanyoyi Yau da kullum.
Ya kara da cewa:kungiyar masu sana,ar siyar da Siminti ta Kasa reshen jihar Kano, a shirye take wajen ganin ta ci gaba da baiwa hukumomin dake da alhakin gyaran titinan jihar Kano gudunmawar da ta kamata domin ciyar da jihar Kano gaba,musamman ta fannonin harkokin sufuri da kasuwancinsu.
Shugabancin kungiyar masu sana,ar siyar da Simintin yace,yana ragewa Gwamnati nauye nauye,musamman wajen Samarwa Matasa ayyukan yi, kasancewar rashin samun ayyukan yi na taka muhimmiyar rawa wajen shigar Matasa ayyukan da busu kamata ba.
/Cov/Ibrahim Sani gama./