Bayan lokaci mai tsawo da aka kwashe ana kada kuri’a a fafatawar da aka yi da ‘yan takara 36, wanda aka watsa kai tsaye a tashar talabijin ta kasar, a farfajiyar majalisar dokokin kasar, tsohon shugaban kasar Hassan sheikh Mohamud ya sami kuri’u 214, sama da adadin da ya ke bukata ya doke shugaba mai ci, Mohammmed Abdullahi Mohammed, wanda ake wa inkiya da Farmajo.
An yi ta harba bindiga sama a babban birnin kasar, Mogadishu, lamarin da ke alamta murnar wannan nasara, inda da dama ke fatan cewa zaben zai kawo karshen rikita rikitar da aka shafe shekara guda ana yi, bayan da wa’adin mulkin Farmajo ya kare a watan Fabrairun 2021 ba tare da an gudanar da zabe ba.
Zababben shugaban Mohamud, wanda ya taba jagorantar kasar daga shekarar 2012 zuwa 2017, ya sha ranstuwar kama aiki jim kadan bayan da aka kammala kirga kuri’un da aka kada, inda daga nan ya gabatar da jawabi ga al’ummar kasar.